Hukumar zaɓe mai zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa a ranar 20 ga Fabrairu, 2027.
Haka kuma, ta ce za a yi zaɓen gwamnonin jihohi da na ‘yan majalisun dokokin jihohi a ranar 6 ga Maris, 2027.
Shugaban INEC, Prof. Joash Amupitan, ne ya bayyana jadawalin zaɓen a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Juma’a.
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan jinkirin amincewa da kudirin dokar zaɓe da aka yi wa kwaskwarima, wanda ke gaban Majalisun kasa domin tantancewa da kuma amincewa.
Tun a ranar 4 ga Fabrairu ne INEC ta bayyana cewa ta kammala shirye-shiryen jadawalin zaɓen da kuma tsarin ayyukan da za a bi, duk da jinkirin da ake samu wajen amincewa da sabuwar dokar.
Hukumar ta kuma ce ta miƙa jadawalin ga ‘yan majalisar dokokin ƙasa, amma ta yi gargadin cewa wasu daga cikin ayyukan da ke cikin jadawalin na iya sauyawa, gwargwadon lokacin da za a dauka kafin amince da kudirin dokar zaɓen da aka yi wa gyara.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t