Da Dumi Duminsa! Hukumar Karota Sun Cimma Matsaya Mai Kyau Da Yan Adai daita Sahu.

Da Dumi Duminsa! 

Hukumar Karota Sun Cimma Matsaya Mai Kyau Da Yan Adai daita Sahu. 

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

Best seller channel ta rawaito, bayan wani zama da kungiyar lauyoyi ta jihar Kano ta NBA ta jagoranta ta re bangarori 3, wato bangaren Gwamnati Baffa Babba Dan-Agundi ya wakilta da  kuma bangaren kungiyar Adaidaita Sahu karkashin jagorancin Alh. Mansur Tanimu da kuma bangaren da Barrister Abba Hikima Fagge yake Wakilta.

A karshe zaman dai a cimma matsaya guda Uku

Best Seller Channel 

1. Kowanne mai Adaidaita Sahu zaiyi Renewal din Permit dinsa akan kudi Naira 5,000 maimakon Naira 8,000 daga yau 19 ga watan January 2022. zuwa  Litinin 28th February 2022. 

Duk wanda ya wuce wannan rana bai biya ba, to zai biya Naira 8,000 maimakon Naira 5,000.

Best Seller Channel 

2. Haka kuma Zaman ya amince da da Biyan Naira 12,000 ga duk wanda zaiyi Sabon Registration maimakon Naira 18,000 daga yanzu zuwa 28th February 2022.

Idan kuma mutum ya wuce Wannan lokacin baiyi Registration ba to zai biya Naira 18,000 maimakon Naira 12,000.

Best Seller Channel 

3. Haka zalika xaman ya amince da cigaba da karbar Naira 100 100 tare tare da biyan Naira 20 a matsayin kudin kungiya.

Kuma zaman ya amince da cigaba da karbar kudin kullum Har ranar Lahadi maimakon Ranar Litinin abiya Naira 200, kuma wannan tsari zai fara aiki ne sati na sama

DA karshe Baffa Babba Dan-Agundi  ya godewa Dricter DSS bisa rokon da ya yiwa mai Gwamna tare da Kungiyar lauyoyi ta jihar Kano karkashin Jagorancin Barrister Sani Gadanya

Slide Up
x