Dubun Wasu Dilolin Wiwi Makare Da Mota Ya Cika A kano
Best Seller Channel
Best Seller Channel
Wata sanarwa da Kakakin yan sandan jihar Kano S P Abdullahi kiyawa ya fitar a ranar Laraba ya bayyana Kama wata mota cike da buhunhunan tabar wiwi a Kano.
Kiyawa ya bayyana kudin tabar Wiwi ya kai Naira Miliyan uku.
An kama tabar wiwin ce a cikin wasu kananan motoci biyu a hanyarsu ta yin safarar zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.
Best Seller Channel
Kiyawa, ya ce, “’Yan sanda masu sintiri ne suka kama su da misalin karfe 3 na dare yayin da suke kokarin ratse.
Mutum na 1 ya zo hannu ne a unguwar Na ibawa, na 2, kuma ya yi kokarin tserewa, amma a hanya ya yi hatsari, aka kama shi a unguwar Birget.
Daya daga cikin fasinjojin motocin da aka kama mai shekara 23, ya ce mutumin da suka dauko wa kayan ya tsere ne ya bar shi, bayan da ya lura cewa za a kama su, bayan sun yi hatsari.
Na yi kokarin tserewa da motar a lokacin da ’yan sanda suka shiga da mu, amma muka yi hatsari a hanya, mai tabar wiwin ya tsere ya bar ni kadai. Inji Yaron motar
Best Seller Channel
Na yi da-na-sanin wannan abu kuma ba zan sake aikatawa ba.
Daya direban kuma, mai shekara 28, ya ce bai san cewa tabar wiwi aka dora masa ba, sai da aka gama lodawa a motarsa. “
Na fito gida ne wani ya kira ni cewa mu je Naibawa Yanlemo akwai kayan da za mu dauka.
Muna zuwa aka yi mana lodin buhunan, ban san cewa tabar wiwi ba ce ba sai da suka gama lodi.
Best Seller Channel
Na ce masa haka bai kamata ba, amma ya ce mu yi sauri mu bar wurin kafin wani abu ya faru.
S P kiyawa yace zasu gurbanar da su gaban kuliya da zarar sun kammala bincike.