Da Dumi Duminsa! Kakakin Rundunar Yan Sanda Kano Ya Samu Karin Girma.

Da Dumi Duminsa! 

Kakakin Rundunar Yan Sanda Kano Ya Samu Karin Girma. 

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

Da yammacin ranar Laraba ne aka hango Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano CP Sama ila Dikko na Makalawa DSP Abdullahi Haruna Kiyawa lambar Karin girma ta S P, wato sufurutandan Yan Sanda. 

Da yake karin bayan kwamishinan ya ce hakan ta biyo bayan jajircewar kiyawa wajen gudanar da aikinsa a jihar Kano. 

Ya kara da cewar wannan shine sakamakon duk wanda ya tsaya tsakaninsa da Allah wajen gudanar da aikinsa. 

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

S P kiyawa da yake nasa jawabin ya fara da cewa. 

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (SWT) Ubangijin talikai.

Na samu karin girma zuwa matsayin Sufurtandan ‘Yan Sanda (SP). 

Ina godiya da addu’o’inku, taimakonku, karfafa gwiwa da kuma hadin kanku. 

Ya kara da cewar, da yardar Allah (SWT), zanci gaba da yin aiki iya kokarina domin tabbatar da kare lafiya da dukiyoyin al’umma.

   Muma daga Best Seller Channel wadda ta koma Alfijir muna taya shi murna Allah ya taya riko ameen summa Ameen

Slide Up
x