Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta fitar da sanarwar shirin rufe dukkan manyan biranen Najeriya daga ranar 15 ga Satumba, 2024.
Alfijir Labarai ta rawaito zanga-zangar za ta biyo bayan karin farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan da kuma rashin iya aiki na Darakta Janar na NNPC, Mele Kyari.
Kungiyar daliban ta bukaci a gaggauta sauya farashin man fetur tare da sauke Mista Male Kyari a matsayin Darakta Janar na NNPC.
Daliban sun shirya mamaye dukkanin manyan biranen kasar a ranar 15 ga Satumba, 2024, kuma sun ba da tabbacin cewa za a gudanar da zanga-zangar cikin lumana da doka
An aike da sanarwar zuwa ga hukumomin tsaro daban-daban, da suka hada da hukumar (NSCDC), da jami’an tsaron DSS, babban hafsan hafsoshin tsaro, sojojin Najeriya, da dukkan gwamnonin jihohi.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj