Ƙungiyar Kwankwasiyya Movement ta sanar da al’ummar Jihar Kano da ma ɗaukacin Najeriya cewa Mataimakin Gwamnan jihar ya miƙa takardar murabus dinsa daga mukaminsa.
A cikin wata sanarwa da kakakin ƙungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed ya fitar, ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin amfanin jama’a da kuma tabbatar da daidaito da kwanciyar hankali a tafiyar da mulki a jihar.
Sanarwar ta ce wasu halin da ake ciki a baya-bayan nan sun kawo cikas ga cikakken aiwatar da ayyuka da nauyin da ke rataye a kan ofishin Mataimakin Gwamna, lamarin da ya sa aka ga ya dace a bai wa ofishin damar yin aiki yadda ya kamata domin amfanin jama’a.
Sai dai sanarwar ta jaddada cewa murabus ɗin bai nuna amincewa da zarge-zargen da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi masa ba. A cewar sanarwar, Mataimakin Gwamnan na nan kan matsayinsa na rashin laifi, yana kuma da yakinin cewa tarihinsa a mulki da hidimar jama’a na nuna gaskiya da jajircewarsa.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa matakin murabus ɗin alama ce ta ƙwarewar shugabanci, da nuna kishin zaman lafiya, balagar siyasa, da kuma gujewa duk wata rikici da ka iya kawo tsaiko ga ci gaban gwamnati da jihar baki ɗaya.
Haka kuma, an bayyana cewa tsohon Mataimakin Gwamnan zai mayar da hankali wajen ƙarfafa ayyukan Kwankwasiyya, da sake gina tsare-tsarenta, tare da shiga muhimman shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027.
A ƙarshe, Kwankwasiyya ta yi kira ga magoya bayanta da al’ummar Kano da su kasance masu bin doka da oda, tare da ci gaba da goyon bayan manufofin dimokuraɗiyya da ingantaccen shugabanci.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t