Da Dumi Duminsa! Sabon Rikici Ya Barke Tsakanin Kwankwaso Da Ganduje a kano.

Sabon Rikici Ya Barke Tsakanin Kwankwaso Da Ganduje a kano.

Best Seller Channel 

 

Best Seller Channel 

A yayin da ake ta raɗe-raɗin yin sulhu tsakanin Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wani sabon rikici siyasa ya sake kunno kai alamun. 

BBC ta ta rawaito cewar kwankwaso yayi wata hira da jaridar Punch a ranar Asabar, in da  ya bayyana yadda Ganduje ya samu a zaɓen 2019 a haramtacciyar hanya, yana cewa wasu gaggan ƴan siyasar jam’iyyar APC ne daga sama suka ƙaƙaba wa al’ummar  Kano shi. 

Best Seller Channel 

Madugun kwankwasiyya ya Kara da cewa muna da abubuwan da za mu iya hana su abun da suka so yi a wannan lokaci, amma sai muka yi la’akari da cewa idan muka bi musu hakan ba zai iya haifar da ɗa mai ido ba, don haka muka barsu da aniyarsu, muka bi matakin shari’a, amma a nan ma aka yi abun da aka yi. 

Sai dai wata sanarwa da ta fito daga fadar jihar Kano mai taken da sa hannun Muhammadu Garba, Kwamishinan watsa labarai ta bayyana kalaman na Kwankwaso a cikin shaci-faɗi da ko kaɗan babu alamun bayyanar gaskiya ciki. 

Gwamnatin ta Kano ta ci gaba da cewa hirar da Kwankwason ya yi da jaridar Punch ta janyo masa illa ne fiye da alfanun da ya yi tsammanin za ta kawo masa. 

Best Seller Channel 

A cewar ta a fili take cewa kwankwaso ya ga ayyukan Ganduje ya tsere wa na sa sa’a wajen wuraren abubuwan ga jama’a, shi ya sa yake ganin ana kokarin shafe abun da yake ganin yayi. 

 ”Kwanan nan aka ji shi ya jan hankalin magoya bayansa su kaucewa furta kalamai amma sai ga shi ya ɓige da yi shi da kansa, ko kaɗan wannan bai dace da shi ba”.

Slide Up
x