Daga Aminu Bala Madobi
‘Yan kasuwar man fetur masu zaman kansu a Najeriya sun bayyana cewa matatar man Dangote da ke tafe za ta ba da Premium Motor Spirit (PMS), wanda aka fi sani da man fetur, a farashin da ya kai N600 zuwa N650 kan kowacce lita.
Bayanai sun ce kungiyar sun yi imanin cewa matatar mai ta Dangote, kamar yadda ta yi da dizal, za ta taimaka wajen rage tsadar man fetur.
Alfijir labarai ta ruwaito mataimakin shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Hammed Fashola, ya bayyana haka a wata hira da jaridar PUNCH cewa, matatar ta dala biliyan 20 za ta iya rage farashin man fetur, matukar ta samu tallafin da ya dace, musamman wajen samar da danyen mai.
Fashola ya bayyana cewa kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), shi kadai ne mai shigo da man fetur, yana sayar wa ’yan kasuwa kan Naira 570 kan kowacce lita. Sai dai da yawa daga cikin ‘yan kungiyar IPMAN suna siya daga masu gidajen ajiya a kan Naira 700 ko sama da haka.
“Mu ‘yan kasuwa ne kuma ko yaushe muna neman mafi kyawun farashi. A halin yanzu muna siya daga NNPC, idan Dangote ya ba da farashi mai rahusa, za mu ci gajiyar sa.
Muna fatan Dangote zai iya bayar da farashi tsakanin N600 zuwa N650 kowacce lita. N600 zai zama karbabben farashi, amma wannan ya dogara da farashin samar da Dangote.
Dangane da farashin man dizal Fashola ya bayyana cewa, “Da farko matatar mai ta Dangote ta rage farashin dizal daga kimanin N1,600 zuwa N1,000. A halin yanzu dai ana saida man dizal kusan N1,150 zuwa N1,200 kowacce lita.
irin wannan farashi zaiyi tasiri akan farashin man fetur, koda yake rikicin danyen mai na yanzu yana haifar da babban kalubale.
Shugaban na IPMAN ya ce kungiyar tana tattauna kan harkokin kasuwanci da wasu jami’an matatar man kan yuwuwar hadin gwiwa, inda ya ce ‘yan kasuwan sunanan suna jiran Dangote.
“Muna kan hanyar tattaunawa. Ina ganin nan ba da jimawa ba za mu kammala tattaunawa,” in ji shi.
Idan za a iya tunawa, a watan da ya gabata ne shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi hasashen cewa matatar man za ta fara aikin hakar mai tsakanin 10 zuwa 12 ga watan Agustan 2024.
Duk da haka, matatar man Mai tace Lita 650,000 a kowacce rana ta gaza fitar da mai a ranar Litinin saboda dalilai daban-daban.
Bincike ya nuna cewa rikicin danyen mai da ke ci gaba da wakana na iya zama koma baya ga matatar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj