Kotun sauraren kararrakin zaben gwamna da ke Kano ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.
Alfijir Labarai ta rawaito cewa dalilan da kotun ta ayyana Gawuna a matsayin wanda aka zaba a matsayin sahihi shine, wadanda aka yi kara na 1 da na 3 sun amince da kada kuri’a.

Don haka kotun ta ce sama da kuri’u dubu 200,000 da mai shigar da kara ke zargi gaskiya ne.
Kotun ta kuma soke wasu daga cikin kuri’un da aka baiwa dan takarar jam’iyyar NNPP, sannan ta cire kuri’u daya daga cikin jimillar kuri’un da ya samu tare da bayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kotun ta soke zaben gwamna Abba Yusuf, inda ta ce ba a zabe shi da mafi rinjayen kuri’u ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb