Ganduje ya mayar da martani kan nasarar APC a jihar Kano

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta A1bdullahi Umar Ganduje, ya mayar da martani kan nasarar da jam’iyyarsu ta samu a kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke jihar Kano.

Alfijir Labarai ta rawaito kotun ta bayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ta kori Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya tsaya takara a jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP).

Ganduje, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar, ya ce bai yi mamakin hukuncin ba, domin ya riga ya san abin da ya faru a lokacin zaben.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da BBC Hausa a ranar Laraba bayan hukuncin kotun.

Na yi matukar farin ciki da hukuncin.

Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki, muna kuma gode wa bangaren shari’a da suka ba da damar yin adalci.

“Ban yi mamaki ba domin duk mun ga abin da ya faru a lokacin zaben. Na biyu, jama’a sun yi ta yi wa jam’iyyar mu addu’a don neman taimakon Allah don mu dawo mana da kujerarmu.”

Dangane da matakin da NNPP ta dauka na zuwa daukaka kara, Ganduje ya ce ita ce cikar dimokuradiyya.

Wannan wani tanadi ne na doka, idan ba ku gamsu ba ku daukaka kara.

Babu laifi a kan hakan, tsarin kasar ya tanadi daukaka kara, kuma za mu hadu a can mutane suna yi mana addu’a.

“Ba mu da tsoro, mun yi imani da Allah, kuma duk wanda ya yi imani da Allah zai samu nasara da yardar Allah,” in ji shi.

Gwamna Ganduje ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da addu’o’in zaman lafiya da ci gaba, inda ya ce tuni sun aza harsashin ayyukan ci gaba a jihar da za su dora a nan gaba.

Muna godiya ga al’ummar jihar Kano nagari, kuma muna ba su tabbacin mun samu kokensu, kuma za mu yi kokarin magance su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

  1. ↩︎

Slide Up
x

One Reply to “Ganduje ya mayar da martani kan nasarar APC a jihar Kano”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *