Dan Wasan Madrid Banzema Ya Lashe kyautar Gwarzon Ɗan Wasan UEFA Na Shekara

Alfijr ta rawaito kyaftin ɗin Real Madrid, Karim Benzema UEFA zabe shi a matsayin gwarzon dan wasan na bana.

Alfijr Labarai

Benzema ya lashe kyautar ne a tsakanin abokin wasansa, Thibaut Courtois da Kevin De Bruyne na Manchester City.

Dan wasan ne ke kan gaba wajen ruwan kwallaye a kakar wasan da ta gabata a gasar zakarun Turai da ƙwallaye 15.

Karim dan kasar Faransa ne, mai shekaru 34 shi ne wanda ake zaton zai lashe kyautar Ballon d’Or, kyauta Mafi daraja a duniyar ƙwallon ƙafa a karshen wannan shekara.

Alfijr Labarai

Dan wasan ya taka rawar gani inda ya bada gudummawar da Real Madrid ta lashe kofin La Liga ta bana, inda ta kare da maki 13 ya kuma, zura kwallaye 35 a wasanni 37 yayin da kungiyar ta kashe gasar La Liga ta bana a ƙarƙashin jagorancin Carlo Ancelotti.

Slide Up
x