Direbobin Dakon Man Fetur A Najeriya Sun Tsayar Da Ranar Fara Yajin Aiki A Fadin Kasar

IMG 20240217 124906

Daga Nasiba Nalado

A Najeriya, ana iya sake fuskantar karancin man fetur, sakamakon alwashin da kungiyar masu motocin haya ta sha na dakatar da dakon man daga ranar Litinin mai zuwa saboda tsadar gudanar da ayyukansu.

Alfijir labarai ta rawaito kungiyar ta sha yin korafi a kan matsanancin tsadar man diesel da ‘yayanta ke amfani da shi wajen aikin dakon man fetur zuwa sassan kasar.

A wata sanarwa da ya fitar a Abuja babban birnin Najeriya, shugaban kungiyar masu motocin hayar, Yusuf Othman ya ce lalai ‘yayan kungiyar za su ajiye motocinsu daga ranar Litinin ta maako mai zuwa.

Othman ya ce hakan ya zama wajibi ne duba da cewa ‘yayan kungiyar na taafka asara a aikin dakon man da suke yi, saboda haka ba za su iya ci gaba da jurewa ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *