‘Yan sanda sun kama mutane 13 da ake zargi da kai hari ofishin yakin neman zaben Sanata Barau a Kano

 ‘Yan sanda sun kama mutane 13 da ake zargi da kai hari ofishin yakin neman zaben Sanata Barau Jibrin a Kano

Rundunar ‘yan sanda ta kama wasu da ake zargin barayin shanu ne da suka kona ofishin Sanata Barau Jibrin, Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa da ke kan hanyar Maiduguri a cikin babban birnin.

 

Solacebase ta ruwaito cewa wasu daruruwa da ake zargin ‘yan bindiga ne a ranar Alhamis din nan sun lalata ofishin yakin neman zaben Sanata Barau Jibrin daga bisani kuma suka far wa wasu mazauna garin. 

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta tabbatar da kama wadanda ake zargin, a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da su. 

 Da samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, ya tashi tare da umurci rundunar ‘Operation Puff Adder’ da su garzaya wurin da lamarin ya faru, suka kuma dawo da zaman lafiya tare da kamo masu laifin. 

 An kama mutane goma sha uku (13) da ake zargin ’yan daba  ne, kuma an kwato  muggan Makamai Masu Hatsari da Gorori da Jarkunan man Fetur. 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi ya yi gargadin cewa, masu aikata laifuka ba za su samu mafaka a jihar Kano ba, ko su tuba  ko su bar Jihar gaba daya. 

Kwamishinan ya kara da cewar In ba haka ba, za a kama su kuma su fuskanci fushin Shari’a. 

Ya godewa al’ummar jihar Kano nagari bisa addu’o’i da karfafa gwiwa da goyon baya da hadin kai, Ya kuma bukaci mazauna yankin da su yi wa Jiha da kasa addu’a tare da kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su kuma kada su dauki doka a hannunsu. 

 DSP ABDULLAHI HARUNA KIYAWA, Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan sanda, a madadin  Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano.

Best seller Channel 

Slide Up
x