Dubun Wani Barawon  Allunan  Maƙabarta Ta Sake Cika A Kano

IMG 20240621 WA0180

Jami’an Bijilante sun kama wani mutum mai suna Bauhari  da ake zargi da satar allunan  Maƙabartar Unguwa Uku dake karamar Hukumar Tarauni Jihar Kano

Alfijir labarai ta ruwaito lamarin ya faru ne da  misalin karfe 3:00 na dare yayin  da Jami’an Bijilante suke gudanar da aikin su gefan makabartar dake kusa da ofishin INEC dake unguwar.

Wanda ake zargi “ya ce  sana’ar sa itace gwan-gwan, Dan  haka ya kan je makabarta dan gudanar da sace allunan alamomi na kaburbura.

Rahotanni na nuni da cewa Al,umma na zargin ƴan gwan-gwan ne ke zuwa su kwashe allunan alamomi na kaburbura.

Sai dai wasu masu sana’ar ta tsince-tsincen kayan ƙarafan wato gwangwan a wannan yankin, sun musanta wannan zargi da ake yi musu.

Jihar Kano dai na da tarin maƙabartu da dama da babu hasken wutar lantarki, abin da wasu ke ganin cewar  wannan kan taimaka wajen bada mafaka ga masu zuwa su aikata miyagun laifuka akicinsu.

A wasu lokuta a baya, an sha samun waɗanda ke shiga maƙabartu a jihar da tsakar dare don tone gawarwaki, su ciri wasu sassan jikinsu dan wata mummunar manufa.

Adamu Abubakar Fiya Fiya Zonal Kwamandan Rundunar Bijilante dake Unguwa uku a zantawarmu da shi ya ce, rundunar  ta samu nasarar cafke mutumin da ake zargin mai suna Bauhari.

Fiya Fiya ya ce bayan samun rahoton  satar allunan  maƙabarta a baya yasa  suke tsaurara Tsaron maƙabartar.

Ya kara da cewar bayan kammala Bincike zamu turasa  wajan  jami’an ƴan sanda domin fadada binciken.

Jaridar Inda Ranka

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *