ji
Alfijr
An kama wani da ake zargin ya kware wajen yin amfani da sunayen maza da mata ta hanyar bude shafukan sada zumunta, don damfarar wadanda tsautsayi ya afkawa, musamman masoya
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano SP Haruna Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi.
Alfijr
An ci gaba da gudanar da bincike wanda ake zargin ya yaudari mutane da dama ta hanyar samun hotuna da bidiyoyinsu na tsiraicinsu inda ya ke barazanar yaɗa su idan suka ki aika masa kudi.
Ayyukan dan damfara a shafukan sada zumunta daban-daban sun bayyana saboda kukan da jama’a ke yi.
Wanda ake zargin dai ya kware wajen yin amfani da sunayen maza, mata, hotuna, da bidiyo, inda ya rika bude asusu daban-daban a Facebook, WhatsApp da damfarar mutane da dama.
Alfijr
Zahra Mansur mai shekaru 20 da haifuwa ta kai ƙara wajen ‘yan sanda, bayan ta samu kiran waya daga makusantan ta cewa wani ya yi amfani da sunanta, hotuna, bidiyo da kuma kirkiro asusun Facebook, wadanda ya yi amfani da su wajen damfarar jama’a da ba su san komai ba.
Rundunar ‘yan sandan bayan ta gudanar da bincike ta cafke wanda ake zargin, Musa Lurwanu Maje, wanda aka fi sani da Social Media da Musa L Maje mai shekaru 26 a kauyen Sitti, karamar hukumar Sumaila ta jihar Kano.
Alfijr
An kama wanda ake zargin yana da wayar hannu Redmi Note 11 Pro. wanda darajarsa ta kai Naira Dubu Dari Biyu da sauran kayan da aka siya daga kudaden da aka samu an kuma kwato kudi naira dubu saba’in, hotuna tsirara da kuma bidiyon wadanda abin ya shafa.
Da ake gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya kware wajen yin amfani da shafukan sada zumunta na bogi wajen damfarar jama’a da ba su ji ba gani ba
Alfijr
Ya yi ikirarin cewa ya kirkiro wani asusun Facebook na bogi mai dauke da sunan ‘’Zahra Mansur’’ kuma yana amfani da hotunanta da bidiyonta wajen damfarar mutane ba tare da izininta ba.
Ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi don gurfanar da wanda ake zargin zuwa Kotu domin girbar abinda ya shuka.