Alfijr ta rawaito karramawar an yiwa Gwamnan Jihar Kano da Mai dakinsa da Mai Dakin Shugaban Kasa, sun samu sarautar a garin Ibadan na Jihar Oyo.
Alfijr
Yayin da aka baiwa Gwamna Ganduje sarautat AARE FIWAJOYE NA IBADAN LAND, an baiwa uwargidan shugaban kasa sarautar YEYE AARE FIWAJOYE NA IBADAN LAND. Mai Martaba Oba Dokta Mohood Olalekan Ishola (Alli OK unmade ll) Olubadan na filin Ibadan ne ya ba wa mutanen biyu sarautar wanda aka gudanar a dakin taro na Mapo Hall, Ibadan, Jihar Oyo.
Taron ya samu halartar manyan baki da suka hada da ɗan takarar shugaban kasa, Alhaji Ahmed Bola Tinubu, da sarakunan Kano, Bichi, Gaya, Rano Karaye, tare da manyan mukarraban gwamnan Kanon da dattijai, ’yan kasuwa, da sauran manyan mutane.