Dungurawa Bashi Da Hurumin Dakatar Da mu, Domin Bashi Ne Halastaccen Shugaban NNPP a Kano — Ina Ji Kawu Sumaila.

IMG 20250224 WA0025

Daga Aminu Bala Madobi

A cikin wata sanarwa Mai dauke da sa hannun maitamaki na musamman ga Kawu Sumaila a harkokin siyasa Babantatu Garko, yace har yanzu sunanan Daram a Jam’iyyar NNPP domin ko basu Dakatu ba.

Sanatan Kano ta Kudu Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila ya ce Sanatan Mas’ud El-Jibrin Doguwa ne halastaccen shugaban jam’iyar NNPP mai kayan marmari a jihar Kano saboda haka Dungurawa bashi hurumin dakatar da shi ko Kabiru Alhassan Rurum ko wani mutu daga jam’iyar NNPP.

“Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa shine doka ta sani a matsayin shugaban jam’iyar NNPP mai kayan marmari kuma itace Jam’iya daya da doka ta sani, saboda haka wani can Dungurawa ya rika kiran kasan a matsayin shugaban jam’iyar NNPP mai Alamar littafi, zancen banza ne, bashi da hurumi, ba shine shugaba ba, saboda haka har yanzu ina jam’iyar NNPP mai kayan marmari,” inji Kawu.

“Lokacin da muka ci zabe bamu san wani Dungurawa a matsayin shugaban jam’iyar NNPP ba, saboda haka bamu da masaniyar wata rana da doka ta amince aka zabi Hashimu Dungurawa a matsayin shugaban jam’iya saboda haka bashi da hurumin ya dakatar da ni, ko Kabiru Alhassa Rurum ko Abdullahi Sani Rogo ko ma Ali Madakin Gini,” inji Sanatan.

“Muna magana ne da yawun Kawu Sumaila, kuma shi mabiyin doka ne saboda haka sanata bai dakatuba, kuma bai san wata jam’iya mai Alamar littafi ba,” inji Shi.

Sanata Sumaila ya bukaci magoya bayansa da kada su tashi hankalin su, yana mai cewa sun dukufa wajen kawo ayyukan raya kasa a kananan hukumomin Kano ta Kudu 16 da ma jihar Kano baki daya.

A gabar da ake cigaba da wannan tankiya cikin Jam’iyyar NNPP, A APCn kano wata Sabuwa ce ta Kunno kai kan makomar shugancin APC a Kano yayin da karamin ministan Gidaje Abdullahi Ata ke nuna yatsa ga Shugabancin Abdullahi Abbas, inda alamu ke nuna nan gaba kadan za a iya kece raini tsakanin jiga jigan Jam’iyyar APCn biyu.

For more information about  Alfijir labarai/Alfijir news follow here  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *