EFCC ta Bankado Kadarori Masu Darajar ₦212bn da Aka Danganta da Abubakar Malami (SAN)

IMG 20251224 WA0327

Daga Aminu Bala Madobi

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta bayyana cewa ta gano kadarori guda 41 da darajarsu ta kai kimanin Naira biliyan 212, waɗanda ake dangantawa da tsohon Ministan Shari’a na gwamnatin Buhari kuma surukinsa, Abubakar Malami (SAN).

Wannan bincike ya tayar da kura a fadin ƙasar nan, inda jama’a ke nuna damuwa kan yadda manyan kadarori ke taruwa a hannun mutum ɗaya.

A Jihar Kano, EFCC ta lissafa kadarori da darajarsu ta kai ₦16,011,800,000, ciki har da Zeennoor Hotel da aka kimanta da ₦11.2bn, Rayhaan Hotel Kano ₦2.24bn, Rayhaan Gym ₦1.225bn, da kuma gidan matar aure a Ahmadu Bello Way mai darajar kusan ₦982.8m.

Sauran sun haɗa da masallaci da tsohon ginin otal, wanda ke ƙara girman jerin kadarorin.

A Jihar Kebbi kuma, an bayyana cewa kadarorin da suka shafi Rayhaan University da bangaren ilimi sun kai darajar ₦162,195,950,000.

Daga ciki akwai filin dindindin na jami’ar ₦56bn, filin wucin gadi ₦37.8bn, makarantu na gaba da sakandare, da sauran gine-gine masu tsada. EFCC ta ce bincike na ci gaba, yayin da ake sa ran matakan shari’a za su biyo baya.

A Abuja Hukumar ta lissafa kadarori na sama da biliyan 34.

Wani Babban Gida duplex Dake Amazon street, Maitama, Mai Darajar 5,950,000,000.00

Meethaq Hotel Jabi Branch
N8, 400,000,000.00

Meethaq Hotel Maitama Branch
12,950,000,000.00

42,units of bungalow A Efab Estate
385,000,000.00

Harmonia Hotel Area 11 Garki

7,000,000,000.00

Wanda Darajar kudin suka tasamma biliyan 212,892,750,000.00

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *