EFCC Ta Kama Akanta-Janar, Ahmad Idris Kan Zargin Badakalar kudade Naira N80bn

Alfijr

Alfijr ta rawaito hukumar yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta kama Akanta Janar na Tarayya (AGF) Ahmad Idris kan badakalar Naira biliyan 80.

Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da kama shi a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Litinin, sanarwar ta ce an kama Ahmad Idris ne bayan da ya kasa amsa gayyatar da hukumar ta yi masa na amsa wasu batutuwan da suka shafi badakalar kudade.

“Hukumar tace ta kama Akanta Janar na Tarayya, Ahmad Idris kan karkatar da kudade da almundahana zuwa Naira biliyan 80 in ji sanarwar.

Alfijr

EFCC tace bayanan sirri da hukumar ta samu sun nuna cewa AGF ta bankado kudaden ne ta hanyar tuntubar juna ta bogi da kuma wasu ayyuka da suka sabawa doka ta hanyar amfani da wasu makusanta, ‘yan uwa, kamar yadda EFCC ta bayyana, an karkatar da kudaden ne ta hannun jarin gidaje a Kano da Abuja.