Daga Aminu Bala Madobi
Mai baiwa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mal. Nasiru El-Rufai a gidansa dake Abuja.
Alfijir labarai ta rawaito Ribadu ya kai ziyarar ne kamar yadda mai taimaka wa El-Rufai, Muyiwa Adekeye ya wallafa a ranar Alhamis.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa tsohon gwamnan na shirin ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa.
El-Rufai ya kai ziyara sakatariyar jam’iyyar SDP ta kasa da ke Abuja, a ranar Laraba.
Wata majiya mai tushe a ziyarar ta shaida wa jaridar Alfijir Labarai cewa ziyarar da El-Rufai ya kai sakatariyar jam’iyyar adawa wadda ta kasance ta zowa kowa da bazata, wanda alamu dake nuni da cewa zai iya ficewa daga jamiyya mai mulkin kasa.
Rahotanni sun ce wannan mataki na da nufin karfafa alakar siyasar sa gabanin zaben 2027 mai zuwa.
Wata majiyar ta kara da cewa tsohon gwamnan ya je ziyarar tuntubar shugaban jam’iyyar SDP na kasa Alhaji Shehu Musa Gabam.
Gabam ya yabawa El-Rufai a matsayin aminin da ke da kwarin guiwa a siyasa, inda ya bayyana cewa Najeriya na bukatar shugabannin kawo sauyi irin sa.
A kwanakin baya ne El-Rufai ya kai ziyarar tuntubar wasu fitattun shugabannin kungiyoyin siyasa daban-daban.
Idan za ku iya tunawa cewa tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) yana kan hanyarsa ta samun nadin mukamai a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a matsayin minista amma aka samu tasgaro ta hanyar cire sunan shi.
Majalisar dattawa ce dai ta gaza tantance shi kan zargin bada kariya ga wasu rukunin jamaa da ake yi masa.
Daga bisani, tsohon ministan ya fita harkar siyasa tareda ta ficewa kasar waje don cigaba da harkokin rayuwarsa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk