Faransa Tace Zata Amince Da Kafa kasar Falasdinu Idan Sun Saki Mutanen Dake Tsare Hannun Su.

IMG 20250922 WA0273

Daga Aminu Bala Madobi

Macron ya kuma yi kakkausar suka kan duk wani shirin korar Falasdinawa daga Gaza

Jaridar Alfijir Labarai Ta Rawaito Cikin wata sanarwa da Emmanuel Macron ya fitar, yace Faransa za ta amince da kafuwar kasar Palastine- muddin mahukunta suka amince da sakin mutanen da suka yi garkuwa da su, inda take adawa da gudun hijirar Gaza

Shirin Faransa na amincewa da kasar Falasdinu ba zai kunshi amincewa da bude ofishin jakadanci ba har sai Hamas ta sako dukkan mutanen da ta yi garkuwa da su a Gaza, in ji shugaba Emmanuel Macron a wata hira da ya gabatar.

Matakin dai ya fusata masu ruwa da tsaki da Isra’ila wadda ke fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan yakin da take yi da kungiyar Hamas a Gaza da kuma lalata shirin jin kai a yankin Gaza da aka yi wa kawanya.

Idan za a iya tunawa a ranar Lahadi ne kuma Portugal ta amince da matsayin Falasdinu, yayin da Faransa ta ce za ta amince da hakan tare da sauran kasashen ranar Litinin a Majalisar Dinkin Duniya.

Macron ya kuma yi kakkausar suka kan duk wani shirin korar Falasdinawa daga Gaza – wanda suke son zama wani bangare na kasa mai cin gashin kanta a nan gaba .

“Gindaya sharuddan irin wannan hauka ne kawai,” in ji Macron.”

“Ba za mu iya yin watsi da irin wannan aikin a fakaice ko a sarari ba.”

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *