
Alfijr ta rawaito Kwamishinan yaɗa labaran Kano Malam Muhammad Garba ya fitar da wata sanarwa, ya ce Kwamitin na ƙarƙashin shugabancin Sakataren Gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji.
Sai kuma wasu Kwamishinoni da manyan jami’an Gwamnatin Kano da kuma wakilci daga ɓangaren zaɓaɓɓen Gwamna.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da zaɓaɓɓen Gwamna ya ƙaddamar da nasa Kwamitin na karɓar mulki.

Jihar Kano dai na cikin jihohin da siyasar ta ke ci gaba da ɗaukar ɗumi kasancewar sauyin Gwamnati da za a yi daga jam’iyya mai mulki zuwa Jami’yyar adawa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Alfijir