Gidauniyar Brotherhood da Better Living Foundation Sun Raba Audugar Mata (SANITARY PAD) KYAUTa ga Daliban Wata Makaranta

1000474509

Gidauniyar Kyautata Rayuwar al’umma  ta Better Living Foundation ta Raba Audugar kariya ga daliban  Makarantar GGASS Dawakin Tofa ranar Laraba 2 ga watan Yuli 2025..

Shirin wanda Gidauniyar ta Kirkiro mai suna BL PAD ME PROJECT wanda Aka Kaddamar a Ranar 16 ga wata Yuni a Makarantar GGSS SHARADA da DALIBAI 250 da Shugaban Kwamitin Amintatattu na Gidauniyar ya Alh Adamu Mukhtar Unguwar Gini ya Kaddamar, an Kirkiro shine don taimakawa Dalibai Mata na Makarantu don kare lafiyarsu daga Kamuwa da cuta da rashin makari mai tsafta ke haifarwa a Lokacin alada..

GGASS Dawakin Tofa ta zamo ta biyu da ta amfana da Wannan tallafi daga Wannan Gidauniya..

A Lokacin raba wannan tallafi Babban Sakataren wannan Gidauniya Ibrahim Ammani ya bayyana cewa wannan shiri zai cigaba da aiwatar da shi a lungu da sako na wannan jiha har sai an cimma Muradin shirin na samawa DALIBAI 5000 AUDUGAR KARIYA a Jihar Kano.

Ya Kara da Cewa Membobin wannan Gidauniya ke hada Kudade don samar da wannan Auduga domin kin kan yaya mata duba da yanayin kaka maka yi da ake ciki.

Sadiya Ahmed Wada Wadda itace Mai Kula da Wannan shiri tayi kira ga Daliban da suka amfana, su yi amfani da abubuwan da aka koya musu a Lokacin wannan taro, kuma suyi amfani da wannan Auduga don kare lafiyarsu.

A nata bangaren Shugabar Wannan Makaranta ta yaba wa wannan gidauniyar bisa Wannan Namijin Kokari, ta kuma yi kira da Sauran Kungiyoyi da su koyi da wannan ƙungiya Wajen irin wannan aiki Musamman a Wannan Lokaci na Matsin Rayuwa.

Abban H. Sani Mainagge
Deputy Director
Media and ICT

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *