Gobara Ta Tashi A Injin Jirgin Sama A Sararin Samaniya Dauke Da Fasinjoji Da Za Su Sauka Lagos

Alfijr ta rawaito wata gobara ta tashi a jirgin sama na Overland Airways.

Jirgin ya yi gaggawar sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagos daga Ilorin a jihar Kwara.

Alfijr

Lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba inda daya daga cikin injinan ya kama wuta a sararin samaniya a lokacin da jirgin ke tunkarar filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagos.

Bisa binciken alfijr ya tabbatar da cewa fasinjoji 33 dake cikin jirgin sun sauka lafiya a filin jirgin sama na kasa da kasa Wing.

Alfijr

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce fasinjojin sun nutsu a duk lokacin da ake gudanar da aikin.

Kamfanin ya ce, “Overland Airways na son sanar da jama’a cewa jirginsa OF1188 daga Ilorin zuwa Lagos ya gamu da wani yanayi mai zafi da ba a saba gani ba a daya daga cikin injinansa a yau Laraba 15 ga watan Yuni, 2022 da misalin karfe 7:50 na dare.

Wannan ya faru ne a lokacin da jirgin ke kokarin sauka, kuma jirgin ya sauka lafiya, ma’aikatan jirgin sun yi kokarin da dabaru don saukar jirgin a tsarinsu na irin wannan yanayi mara kyau.

Alfijr

Sanarwar ta kara da cewa dukkan fasinjoji 33 sun nutsu a cikin wannan yanayi da jirgin ya shiga, kuma sun sauka lafiya lau bisa ka’idojin COVID-19 bayan Jirgin ya tsaya a filin jirgin saman Murtala Mohammed na Lagos.

Babu wani fasinja da ya ji rauni ta kowace hanya. “Overland Airways na jinjinawa kwararrun hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya (FAAN), hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NAMA), hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA) da kuma Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (AIB-N) wadanda suka yi gaggawar da kuma kwantar da hankula.

Alfijr Babu wani fasinja da ya ji rauni ta kowace hanya. “Overland Airways na jinjinawa kwararrun hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya (FAAN), hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NAMA), hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA) da kuma Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (AIB-N) wadanda suka yi gaggawar da kuma kwantar da hankula.

Alfijr

Overland Airways ya yi nadamar duk wani rashin jin daɗi ga fasinjojinsa kuma yana ba da tabbacin jama’a masu balaguro da cikakken alƙawarinsa na kiyaye ayyukansa da fasinjoji.

Slide Up
x