Alfijr ta rawaito akalla mutum daya ya mutu tare da lalata gidaje 32 bayan wata iska da ambaliyar ruwa a kauyen Yan Tsagai da ke karamar hukumar Rano a jihar Kano.
Dr Sale Jili, Babban Sakataren Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta (SEMA) ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Alhamis a Kano.
Alfijr
Jili ya ce mutane da dama kuma sun rasa matsugunansu sakamakon bala’in da ya afku a ranar 4 ga watan Yuni. “Wasu daga cikin mutanen da suka rasa matsugunansu na samun mafaka tare da ‘yan uwansu a cikin jama ar da abin ya shafa, yayin da wasu kuma suka fara sake gina gidajensu,” inji shi.
Jili ya ce hukumar ta tura jami’anta zuwa ga al’umma domin tantance irin barnar da aka yi domin shiga tsakani. “Mun ziyarci kauyen ’Yan Tsagai tare da raba kayan agaji ga wadanda abin ya shafa a matsayin matakan rage musu radadi.
Alfijr
“Kayayyakin da aka raba sun hada da buhunan shinkafa 30, buhunan masara 30, buhunan wake 30, buhunan siminti 30, kwanan rufi da kusoshi.
Sauran kayayyakin sun hada da bokitin roba, cokali, kofuna, kayan lambu, matashin kai, katifa, tumatir da gwangwani da kayan yaji,” in ji shi.
Alfijr
Ya shawarci mazauna yankin da su rika tsaftace magudanan ruwa tare da kaucewa gina gidaje a magudanan ruwa domin gujewa ambaliyar ruwa.
Kamar yadda Solacebase ta wallafa