Gwamnan jahar kano Abba Kabir Yusuf ya ziyarci gidan marayu dake kofar nasarawa tare da kwomishinonin sa daga ciki Akwai kwamishiniyar mata Hajiya Aisha Saji da Kwamishinan yada labarai na jahar kano hon baba halilu Dantiye MNI FNGE MON.
Gwamna Yaci Abinci tare da marayun sannan yayi kira ga sauran al’umma suyi koyi da hakan domin shi ‘da nakowa ne.
A nata bangaren Kwamishinar Mata ta jihar Kano Haniya Aisha Saji itama ta ja hankalin Iyaye mata wajen rke amanar da aka bar musu ta ya’ya cikin aminci saboda kema zata iya zuwa kanki.
Ku sani iyaye mata amace fa Allah ya bamu don haka muji tsoransa domin zamu tsaya gabansa mu girbi abinda muka shuka.
Sannan gwamnan ya raba musu kayan Abinci da lemuka da ruwan Sha da dai sauran kayayyaki.




















Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj