Gwamnan Kano ya buƙaci a binciki Ganduje kan rage kuɗaɗen tsofaffin ma’aikata

FB IMG 1719762772263

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya roƙi a yi bincike kan zargin rage kuɗaɗen giratuti na tsofaffin ma’aikata ƙarƙashin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Alfijir labarai ta ruwaito a lokacin da ya ke jawabi a bikin ƙaddamar da zango ba biyu na biyan giratuti da na ma’aikatan da suka mutu, Abba ya ce akwai Naira biliyan 5 da aka rage na ƴan fansho mutum 4,000 cikin kuɗin wanda babu bayanai a kan su, don haka ya buƙaci hukumar da ke da alhaki a kai, ta yi bincike.

Abba ya shawarci ƙungiyar ƴan fansho ta ƙasa (NUP), da ta shigar da ƙara kan haka wa gwamnatin jihar, inda ya tabbatar da cewa za a gudanar da bincike tare da zartar da hukunci a kan duk wanda aka samu da hannu a cikin sauya akalan kuɗaɗen.

Gwamnan ya ƙara da cewa, gwamnatinsa a zango na farko ta biya Naira biliyan 6 wanda ya zama jimillar biliyan 11, sannan kuma su na cigaba da ƙoƙarin warware matsalar biyan ƙuɗin ma’aikatan wanda ya kai biliyan 40 da ba’a biya su ba inda ya alƙawarta mu su da iyalan waɗanda aka rasa cewa za a bai wa kowa haƙƙinsa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *