Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Kar-ta-Kwana Don Tunkarar Matsalolin Tsaro a Fadin Jihar

Abba k Yusuf

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta kafa wani kwamitin kar-ta-kwana domin tunkarar barazanar tsaro da ke kara ta’azzara a tashoshin motoci da sauran wuraren taruwar jama’a a faɗin jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan kara yawaitar ayyukanb laifuka a wasu muhimman wurare, musamman a tashar mota ta Kofar Ruwa, inda aka kama wasu da ake zargi da aikata laifi.

Kwamitin zai mayar da hankali wajen sanya idanu da gudanar da bincike, da kuma tsara dabarun tsaro a wuraren da ake zargin ana aikata laifuka, ciki har da tashoshin mota, gidajen mai, da sauran wuraren da jama’a ke taruwa.

Gwamna Yusuf ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gaggawa da gwamnatinsa ke dauka domin dakile barazanar tsaro tun kafin ta kazanta.

Haka kuma, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *