Gwamnan Kano Ya Nada Kwamitin Riko A Kasuwar Waya ta Farm Center

FB IMG 1695680993148

Gwamnatin jihar kano ta amince da nada kwamitin riko na kasuwar sayar da wayar hannu ta Farm Center dake jihar.

Alfijir labarai ta rawaito kwamishinan kasuwanci na jihar Kano Alhaji Abbas Sani Abbas ne ya jagoranci bikin rantsar da sabbin shugabannin kwamitin rikon kasuwar a yau juma’a.

Ga jerin Sunayen Sabbin shugabannin kwamitin

AbdulMalik Garba Zango( Chairman)

Amb Jamilu Bala Gama (Secretary General)

Abdulaziz Badamasi (Member)

Jamilu Ahmad Mashalo
(Member)

Nura Bakwankwashe (Member)

Sagiru Abubakar (Member)

Tijjani Uba Ibrahim
Member

Kwamishinan ya bukaci sabbin kwamitin rikon kasuwar ta Farm Center da su zamo masu gaskiya da riko, sannan su zauna da mutane lafiya tare da kawo abubunwan da zasu ciyar da kasuwar gaba.

” Gwamnatin Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf ta damu da sosai da harkokin Kasuwanci don haka yayi tanade-tanaden masu tarin yawa domin bunkasa harkokin Kasuwanci a jihar Kano, kasancewar ta cibiyar Kasuwanci”.

Da yake zantawa jaridar kadaura24, Babban Sakataren kwamitin rikon kasuwar ta Farm Center Amb. Jamilu Bala Gama ya bada tabbatacin zasu yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun ciyar da kasuwar gaba.

” Muna da tsare-tsaren masu yawa wadanda idan muka fara aiwatar da su zasu kawo cigaba a kasuwar, sannan zamu yi kokarin zamanantar da harkokin waya a kasuwar. Don haka muna neman hadin kan yan kasuwar da masu zuwa siyayya don mu sami damar Aiwatar da manufofin mu”.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *