Gwamnan ya umarci Ma’aikatar Lafiya ta Kano da ta tabbatar an ba dukkan waɗanda hatsarin ya rutsa da su kulawar lafiya kyauta
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matuƙar alhininsa kan mummunan hatsarin mota da ya rutsa da wasu mutane a safiyar Lahadi a Kwanar Barde, ƙaramar hukumar Gezawa, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar fiye da mutum 30.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi mai raɗaɗi, ba ga iyalan waɗanda abin ya shafa kaɗai ba, har ma ga al’ummar Jihar Kano baki ɗaya.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya rutsa da wata babbar mota (tirela) da ke kan hanyarta zuwa Gujungu, wadda ake zargin direbanta da tuƙi cikin sakaci, inda ta yi taho-mu-gama da wata motar haya mai ɗaukar fasinjoji.
Yayin da fiye da mutane 30 suka rasa rayukansu, wasu da dama sun jikkata.
Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan mamatan, tare da rokon Allah Ya bawa waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa.
Gwamnan ya umarci Ma’aikatar Lafiya ta Kano da ta tabbatar an ba dukkan waɗanda hatsarin ya rutsa da su kulawar lafiya kyauta, sannan ya gargadi direbobin manyan motoci da su guji tukin ganganci domin kare faruwar irin hatsari a gaba.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t