Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tafi Amurka don yin kwas kan harkokin mulki.
Best Seller Channel
Best Seller Channel ta rawaito a wata Sanarwa da Mal Muhammad Garba kwamishin yada labarai na Gwamnatin Kano ya sanar da manema labarai a ranar Talata cewat Ganduje ya halarci shirin jagoranci a Amurka, ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa Dr Nasiru Gawuna.
Best Seller Channel
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya tafi kasar Amurka inda yake halartar wani shiri na tsawon mako guda.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa Gwamna Ganduje na halartar wani shiri na inganta jagoranci na kwarai a makarantar kasuwanci ta Harvard da ke Boston.
Ya ce gwamnan ya mika mulki kuma ya ba mataimakin gwamna Dakta Nasir Yusuf Gawuna cikakken wa’adin zama mukaddashin gwamnan jihar.
Sanarwar ta kara da cewa duk wata hada-hadar kasuwanci a hukumance daga yanzu sai an bi ta ofishin mataimakin gwamna domin daukar matakin da ya dace. .
Best Seller Channel
Sanarwar dai MALAM MUHAMMAD GARBA Hon. Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano shine ya saka Mata hannu