Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tsige sakatarorin dindindin da daraktoci a ofishin Mataimakin Gwamna da kuma ma’aikatar kananan hukumomi. Wannan mataki ya biyo bayan rikicin cikin gida da ke faruwa a jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar.
Alfijir labarai ta rawaito rahotanni sun bayyana cewa matakin na gwamnan ya zo ne don gyara tsare-tsaren shugabanci tare da tabbatar da cewa ana samun daidaito da nagartar aiki a tsakanin bangarorin gwamnati.
Wannan yana zuwa a wani lokaci da ake samun matsaloli tsakanin bangarorin jam’iyyar NNPP da kuma shakku a kan yadda ake tafiyar da lamuran siyasa a jihar.
Haka zalika, wasu majiyoyi sun nuna cewa wannan tsige-tsigen na iya zama wata hanya ta rage tasirin wasu kusoshin gwamnati wadanda ake ganin suna da hannu wajen haifar da rikice-rikicen cikin gida.
Daily Nigerian
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj