Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Baiwa kwamitin Hisbah Tallafin Miliyan Dari N100m

Alfijr ta rawaito Gwamnatin jihar Kebbi ta baiwa kwamitin Hisbah na jiha tallafin naira miliyan 100 da aka kafa shekaru 20 da suka gabata domin bunkasa kyawawan dabi’u da magance matsalolin zamantakewa a tsakanin al’umma.

Alfijr Labarai

Gwamna Atiku Bagudu ne ya sanar da bayar da tallafin a ranar Lahadi a Birnin Kebbi a yayin wani taron tara kudade na kwamitin a wani bangare na ayyukan bikin cika shekaru 20 da kafuwa.

Kwamitin Hisbah ya yi fatan tara Naira miliyan 120 domin ayyukan ta.

Bagudu ya ce gwamnatin jihar da ‘yan majalisar dokoki da kuma kananan hukumomi 21 ne suka bayar da gudunmawar kudin tare da hadin gwiwa.

Dole ne mu amince da gagarumar gudunmawar da Hisbah ke bayarwa wajen cusa kyawawan dabi’u a cikin ‘yan kasa.

Alfijr Labarai

Gudunmawar ta hada da shiga ayyukan jin dadin jama’a da yaki da matsalolin al’umma kamar shaye-shayen barasa da karuwanci, warware rikicin aure da dai sauransu.

Kungiyar ta kasance a sahun gaba wajen hana aikata laifuka a cikin al’umma, saboda tsarin da take bi na dakile munanan dabi’u da miyagun laifuka, gwamnati mai ci ta hada da hukumar Hisbah a cikin injunan tsaro na jihar,” inji shi.

Gwamnan ya yabawa gwamnatocin baya da suka kafa kwamitin na Hisbah da kuma ci gaba da rikewa, sannan ya yabawa shugabannin da mambobinsa bisa jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Babale Umar-Yauri wanda ofishinsa ne ke sa ido kan kwamatin Hisbah ya bayyana cewa kwamatin ya taka rawar gani a cikin shekaru 20 da suka gabata.

Alfijr Labarai

Wadannan nasarorin sun hada da rufe wuraren shan giya, gidajen karuwai, ceto yaran da aka yi watsi da su da jariran da aka haifa da sauran ayyukan agaji, wadanda su ne alamar ayyukan Hisbah a jihar,” inji shi.

Umar-Yauri ya godewa gwamnan kan yadda ya ci gaba da tallafa wa kwamitin kudi da kuma biyan kudin shirya bikin cika shekaru 20.

Tun da farko, mai rikon mukamin Khadi na jihar, Dakta Muhammad Argungu, ya bayyana bikin nasarorin da hukumar ta Hisbah ta samu cikin shekaru 20 da kafuwa, a matsayin abin alfahari.

Hukumar Hisbah ta bayar da gudunmawa sosai wajen tsaftar al’umma da kawar da abubuwan da ke da illa ga lafiya da rayuwar jama’a,” inji shi.

Argungu ya godewa Bagudu bisa kulawarsa a matsayin uba ga marayu a jihar.

Alfijr Labarai

A nasa jawabin, Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Bashar, ya jaddada aniyar Masarautar Gwandu na tallafawa da bayar da hadin kai ga kwamitin Hisbah wajen inganta rayuwar al’umma, bisa tsarin addinin Musulunci.

Sarkin wanda ya samu wakilcin Walin Gwandu, Sheikh Mukhtar Abdullahi, ya shawarci al’umma da su marawa kwamitin Hisbah baya domin gudanar da aikin da ya dace na tsarkake al’umma daga dukkan munanan dabi’u.

Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami (SAN) ya amince da ayyukan kwamitin, inda ya ce ya taimaka wajen rage shaye-shaye da karuwanci a jihar.

Malami wanda ya jagoranci taron, ya shawarci kwamitin da ya maida hankali wajen magance shan wasu abubuwan maye a tsakanin matasa.

Alfijr Labarai

Tsohon Kwamishinan Ayyuka da Sufuri, Abubakar Chika-Ladan, ya wakilce shi, ya yi gargadin cewa dole ne a magance karuwar shan miyagun kwayoyi ta hanyar aika sako domin ceto makomar matasa da kuma illar da ke haifarwa ga al’umma.

Ministan ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 5 ga kwamitin Hisbah yayin da dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC, Dr Nasir Idris ya bayar da Naira 500,000.

(NAN)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *