Alfijr ta rawaito Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyar NNPP Abba Kabir Yusuf ya yi karar gwamnatin Kano Abdullahi Umar Ganduje a gaban wata kotu bisa siyar da filin wasa na mahaha da kuma katangar filin wasa na Sani Abacha dake unguwar kofar mata.
Alfijr Labarai
Abba Kabir ya shigar da karar ne karkashin wasu lauyoyi, inda ya zargi gwaman da cefanar da wasu kotunan musulunci biyu a nan Kano.
Sauran wadanda ake karar sun hada da kwamishinan shari’a na jihar Kano da hukumar kasa da safayo.
Da ya ke zantawa da Premier Radio a madadin Abba Kabir Lauyansa Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzurci ya zargi gwamnan da cefanar da wuraren ne saboda son rai da biyan bukatar kansa
Alfijr Labarai
Ya ce gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje na wuce gona da iri wajen siyar da irin wadannan wurare masu amfani ga al’ummar jihar Kano.
Baya ga wannan kuma masu karar sun yi korafi kan siyar da wasu kotunan shari’ar musulunci zuwa ga wasu dai-daikun mutane, wanda shima suke ganin hakan ya sabawa dokar kasa.
Masu karar dai sun shigar da ita ga babban babban mai shari’a na Kano, Justice Nura Sagir, wanda kuma ya sanya ranar 10 da 11 ga Nuwamba domin fara sauraran karar.
Premier Radio
Ya Allah Kai Mana maganin wadannan abubuwa mararsa dadin ji a jihar mu kano.Abba k Yusuf Allah ya shiga lamarin ka ya Dora ka da du yan takarar NNPP akan kujerun ku Dan Sayyidina Rasulullah Saw.
Allah ya bamu gwamna mai kishin al ummar jihar kano
Ameen ameen