Daga Aminu Bala Madobi
Biyo bayan mataki da shugabannin kafafen yada labarai na jihar kano suka dauka na dakatar da gabatar da shirye shiryen siyasa na wucin gadi, a yunƙurin tsaftace tsarin.
Kan wannan mataki, wasu masu sharhi na kallon yunƙurin tamkar dakile tanadin doka sashi na 39
Gwamnatin jihar Kano ta ce bata da wani shiri ko kuma yunkuri na hana wasu mutane yin adawa ko kalubalantar gwamnati ba, fa ce kawai tafi maida hankali wajan yin siyasa ta mutuntaka, mai tsafta ba tare da cin zarafin kowa ba.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu da ma’aikatar yada labarai ta shiryawa masu yin amfani da kafafen sada zumunta, dan su kara tsaftace aikin su.
Waiya ya kuma ce, da yawa wasu suna yada labaran ƙage dan samun mabiya wanda a cewar sa hakan ba dai-dai bane.
Tunda farko da yake jawabi masani a harkokin yada labarai kuma malami a tsangayar koyar da aikin Jarida na Jami’ar Bayero dake nan Kano Farfesa Sule Ya’u Sule jan hankalin masu amfani da kafafen yada labarai ta hanyoyin sadarwar Internet ya yi da su rinka wallafa labarin da yake na hakika ba tare da kage ba.
Masana aikin jarida da yada labarai da dama ne dai suka gabatar da makala kan muhimmancin yada labarai sahihi domin amfanar al’umma.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD