Hakan ta faru ne bayan wani zaman sulhu da Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida camarade Ibrahim Abdullahi Waiya ya kira wo a yau Laraba domin daidaita al’amuran da suka lalace.
Taron sulhun ya samu halartar shugabannin yan jarida na yanar gizo Kano Online Media Chapel, karkashin jagorancin shugabanta, Comrade Abubakar Abdulƙadir Dangambo, da daraktocin ma’aikatar yaɗa labarai, tare da dan jarida kuma tsohon shugaban NUJ, Comrade Abdullahi Datti Arzai.
Da yake jawabi a yayin taron, Kwamishina Waiya ya bukaci SSR Rogo da sauran jami’an gwamnati da su rika kyautata alaka da ’yan jarida domin ci gaban jihar.
Ya kuma jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da aiki kafada da kafada da kafafen yada labarai, yana mai amincewa da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen wayar da kan al’umma kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
A nasa bangaren, Shugaban Kano Online Media Chapel, Comrade Abdulƙadir Dangambo, ya gode wa kwamishinan bisa saurin shiga tsakani da ya yi wajen warware matsalar duba da dama shi Rogon ya dade yana irin wannan halayyar ga ƴan jarida ba wannan ne farau ba.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, tare da jan hankalin jami’an gwamnati da su fahimci rawar da ’yan jarida ke takawa a cikin al’umma da irin mahimmancin da suke dashi.
Wannan yazone a gabar da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na ciki da wajen kasarnan suka yi Allah wadai da faruwar lamarin tare da bawa gwamnatin jihar Kano wa’adin sa’o’i 24, su dauki mataki ko suhadu a gaban kuliya.
Muna fatan wannan sulhun da aka yi ya da ya gyara halayyarsa da mutane, domin wannan ba shine farau a gareshi ba.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t