Daga Rabi’u Usman
Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan hukumomin kano dasu tabbatar da sunyi aiki me inganci kamar yanda suka yi alkawari na tsawon shekaru 20 tare da gujewa bayar da na goro wajen bibiyar takardun kwangila.
Alfijir labarai ta rawaito Kwamishinan kananan hukumomin kano Hon Muhammad Tajo Usman ne ya bayyana hakan yayin da ‘yan kwangilar suka kai ziyarar aiki ofishin sa dake ma’aikatar kananan hukumomin kano.
Yana mai cewar, kafin a bayar da wani aiki a gwamnatance, an ajiye kudin da za’a biya ‘Dan Kwangila hakkin sa.
Ya kara da cewa, ba’a yarda wani Dan Kwangila ya dinga zuwa ma’aikatar kananan hukumomi domin bibiyar File dinsa ba domin gudun rashawa a tsakanin ma’aikata da Dan Kwangila.
*Haka kuma akwai sabuwar ma’aikata ta musamman da gwamnatin kano ta Samar da zata dinga bibiyar aikin da aka bayar daga kananan hukumomin kano domin tabbatar da nagartar ayyukan da aka basu – “_inji kwamishinan”_*
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan fitowar su, Shugaban kungiyar ‘yan kwangilar ayyukan kananan hukumomin kano 44 *(Association of 44 local government contractors of Nigeria Kano State Branch)* Alhaji Rabiu Aliyu Kiru.
Ya jaddada aniyar su na kora da kuma gurfanar da duk wani Dan Kwangila daga cikin mambobin su da yayi aiki mara Inganci tare da sabunta aikin da aka bashi ba tare da an sake biyan kudin aikin ba.
Ya kara da cewa, tuni dai shirye shirye suka yi nisa wajen fara ayyukan kananan hukumomin kano 44 domin sabunta jihar kano da manya manyan ayyukan gwamnatin kano.
Wakilin mu ya ruwaito cewar daga cikin mambobin kungiyar ‘yan kwangilar sun Mika Godiya ga gwamnatin kano bisa jajircewar ta na tabbatar da sabunta kano ta hanyar aikace aikacen a kananan hukumomin kano 44.
Wadanda suka hadar da, Gina tituna, Gyaran makarantu, Gina Famfunan burtsatse na tuka tuka da masu aiki da hasken rana, asibitoci da dai sauran su.
Idan dai ba’a manta ba, a karshen makon da mukayi ban kwana da shi kungiyar yan kwangilar sunkai ziyarar neman goyon bayan shugabannin kananan hukumomin kano 44 karkashin jagorancin shugaban rikon shugabannin kananan hukumomin Hon Jamilu Abubakar Dambatta.
Inda ya basu tabbacin yin aiki tare domin tabbatar da kudirin gwamnatin kano na sabunta kano ta hanyar manya manyan ayyukan raya kasa.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ