Gwamnatin Kano Ta Kafa Sabbin Dokokin Gudanar Da Hotels, Event Center, Gidan Abinci da Kuma Suya Spot
Best Seller Channel
Best Seller Channel
Best Seller Channel ta rawaito, kwamitin tabbatar da biyan kudin harajin gidajen saukar baki da na shakatawa da guraren gudanar da bukukuwa da yawan buda Ido na Jihar Kano, karkashin Jagorancin shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Dan-Agundi da shugaban hukumar shakatawa Da yawon bude idanu ta Jihar Kano Hon Yusuf Ibrahim Lajawa sun gana da masu Hotel da guraren shakatawa dana Bukukuwa Sama da dari biyar (500) dan sanar dasu sabuwar dokar biyan kudin harajin guraren sana’o’insu da kuma tsaftace guraren dan tabbatar kawar da aiyukan Badala a jihar Kano.
Kwamitin an kafa shine a karkashin wata doka ta yawan bude idanu ta jihar Kano ta Shekarar 2021.
Best Seller Channel
Tanadin Tsaftace Hotels a kano.
Kwamitin zaiyi aikin tabbatar da hana shigar kananan yara yan kasa da Shekara goma sha takwas (18) cikin Hotel ba tare da iyayen su ko shakikansu ba.
Hana Shan Shisha, da wanka a Swimming pool maza da mata, kawar da aiyukan Luwadi da Madigo a jihar.
Best Seller Channel
Tsaftace Event Centres a kano.
Dole masu event su kashe Sauti na minti 15 zuwa Sama a lokacin gudanar da Sallar Magariba da Sallar Isha”I.
Kuma ya zama wajibi tashi a guraren bukukuwa kafin karfe goma sha daya na dare, tabbatar da’a tare hanyar wucewar jama’a, da kuma waje jinsi.
Best Seller Channel
RESTAURANTS & SUYA SPOT
Tabbatar da tsaftar wajen Sana’a da kuma tabbatar da lafiyar ma’aikatan dake aiki a guraren siyar da Abinci ko kayan makulashe.
Sannan tabbatar da ingancin Abincin da za’a bawa mai siya da kuma tabbatar da cewar yawan cin wannan abinci bashi da matsala ga rayuwarsa,
Shugaban Hukumar Shakatawa Da yawan bude ido ta Jihar Kano Hon Yusuf Ibrahim Lajawa ya kara Kira a babbar murya ga masu gudanar da wadannan sana oi da su ji tsoran Allah wajen tsaftacewa da bin dokokin don cigaban jaharmu da hadu da Allah Lami lafiya.
Best Seller Channel
Bayan kammala wannan tattaunawar mai girma Gwamnan jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ƙaddamar da motocin aiki na wannan Kwamitin, inda ya tabbatar da bayar dukkanin goyan bayansa dan tabbatar da Nasarar aikin Kwamitin.
.