Gwamnatin Kano Ta Magantu Akan Zargin Da Ake Mata A Shari’ar Murja Kunya

FB IMG 1695680993148

Gwamnati tana sane da cewa batun na doka ne da yake cikin tsarin shari’a kuma ba za ta taɓa yin katsalandan ta kowace hanya don yin tasiri wajen samar da Rashin adalci ba.

Alfijir labarai ta rawaito Gwamnatin Jihar Kano ta ce ba za ta yi katsalandan a cikin shari’ar da ake yi wa fitacciyar ƴar Tiktok din nan Murja Kunya ba.

“Sai dai an shaida wa gwamnati cewa an sake samun wani sabon zargin da ake yi mata wanda ya sa jami’an tsaro suka fitar da ita daga gidan gyaran halin domin bincike” a cewar sanarwar mai ɗauke da sa hannun Kwamishina Watsa Labarai, Baba Halilu Dantiye a ranar Litinin.

Gwamnatin ta ce ta fitar da sanarwar ce saboda “An jawo hankalinta kan wani zargi mara tushe da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta kan cewa da hannunta a sakin Murja Ibrahim Kunya da aka yi daga gidan yari, wacce take fuskantar shari’a a kan watsa bidiyon da suka take wasu dokokin jihar.”

Sanarwar ta ƙara da cewa “waɗannan zarge-zarge kwata-kwata ba su da tushe balle makama, ba gaskiya ba ne, wani hasashe ne marar tushe na wasu ɓata-gari da suke so su baƙantawa gwamnati a idon al’umma.

A makon da ya gabata ne Hukumar Hisbah a Kano ta kama Murja Ibrahim Kunya inda har ta gurfanar da ita a gaban kotu bisa wasu zarge-zarge da suka haɗa da yin bidiyon rashin tarbiyya a kafafen sada zumunta.

Kotun ta tura ta gidan gyaran hali da niyyar zuwa ranar da za a koma sauraron shari’ar, amma daga baya hukumar gidan yarin ta sake ta bayan da ta ce ta samu takardar daga kotu.

Gwamnatin jihar ta ce tana sane da tanadin da kundin tsarin mulkin kasar ya yi na raba madafun iko da ma’auni tsakanin bangaren shari’a da na majalisa da na zartarwa a matsayin bangarori uku na gwamnati, kuma ba za ta taɓa yin wani abu da zai kawo cikas ga wannan tsari ba.

Gwamnati tana sane da cewa batun na doka ne da yake cikin tsarin shari’a kuma ba za ta taɓa yin katsalandan ta kowace hanya don yin tasiri wajen samar da Rashin adalci ba.

Sanarwar ta kuma tunatar da al’umma cewa abin da ta sani a kan batun shi ne cewa an gurfanar da Murja Kunya a gaban wata Kotun Shari’a da ke Kwana Hudu a karamar hukumar Nassarawa bisa zargin ta da yada wasu munanan bidiyoyi a dandalin sada zumunta, inda kotu ta bayar da umarnin hakan tare ta a gidan gyaran hali kafin a ci gaba da sauraron shari’ar a ranar Talata, 20 ga Fabrairun 2024 bayan ta saurari bukatar neman belinta.

A ƙarshe gwamnatin ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da zargin da ake yi mata, tana cewa ba wani abu ba ne illa ƙoƙarin ɓata mata suna tare da tabbatar wa al’ummar jihar cewa za ta ci gaba da mutuntawa tare da kiyaye alfarmar tanadin kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *