Kotu Ta Yankewa Princess Ramlat Hukuncin Zaman Gidan Yari

IMG 20240219 212323

Kotun Muslunci ta yanke hukuncin zaman gidan yari ga Ramlat ’yar TikTok wadda ta bayyana kanta a matsayin ‘yar madigo

Alfijir labarai ta rawaito Kotun Muslunci da ke unguwar Sharada a Jihar Kano ta yanke hukuncin dauri a gidan yari ga matashiyar ’yar TikTok, Ramlat Muhammad.

Kotun ta yanke wa Ramlat hukuncin ne kan samun ta da laifin badala, fitsara da kuma yawon ta-zubar.

A yammacin wannan rana ta 19 ga Fabrairu 2024 Mai Shari’a Sani Tanimu Hausawa na ya yanke wa Ramlat hukuncin dauri na tsawon wata bakwai da zabin biyan tarar Naira 50,000.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce ta gurfanar da ita kan laifuka kamar haka:

1- Fitsara da rashin tarbiyya da yada ɓaɗala

2- yawon banza da ta zubar

3- Fitsara wanda ya saba da sashe na 385.

A tuhumar farko alkalin ya yanke wa Ramlat hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata uku ko zabin tara ta Naira dubu talatin.

Sai laifin yawon banza, wanda a kansa alkalin ya yanke mata hukuncin daurin wata uku a ko zabin tara na Naira 20,000.

A laifi na uku da aka kama ta da shi na fitsara kuma alkalin ya yanke mata hukunci bisa sassauci da ta nema zaman gidan yari na tsawon wata guda babu zabin tara.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *