Gwamnatin kano ta shirya sayo Jirage marasa matuka don yakar yan bindiga

FB IMG 1764772548155

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin gwamnatin sa na siyo jirage marasa matuka da kayan aiki na sa ido da saurin mayar da martani domin kare mazauna iyakokin Kano da Katsina daga hare-haren ’yan bindiga.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya turawa manema labarai a yau Laraba.

Wannan ya zo ne yayin da gwamnan ke duba shirin Joint Task Force (JTF) wajen tunkarar hare-haren kwanan nan a kananan hukumomin Tsanyawa da Shanono, inda aka sace mutane kimanin 5 a Tsanyawa da 10 a Shanono, ciki har da mace guda da ta rasa rayuwarta.

Gwamna ya roki mazauna yankunan da su ba da bayanai masu amfani kan motsin ’yan bindiga, sannan ya umarci JTF da su yi iyakar ƙoƙarinsu wajen kubutar da wadanda aka sace.

Hakazalika ya tabbatar wa dakarun da iyalan da abin ya shafa cewa gwamnati na yin iyakar ƙoƙarin ta wajen mayar da wadanda aka sace ga iyalansu cikin kankanin lokaci.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *