Gwamnatin Kano Ta Soke Karin Wa’adin Ma’aikan Jihar 4,000 Da Ganduje Yayi

FB IMG 1723959647845

Aƙalla ma’aikan jihar Kano 4,000 da gwamnatin tsohon gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ta tsawaita wa wa’adin  aiki ne ake sa ran za su ritaya a ranar 1 ga Disamban 2024.

Alfijir Labarai ta rawaito gwamnatin jihar ta ce ta kammala bincike da tantace ma’aikatan, waɗanda aka yi wa ƙarin wa’adin aiki bayan sun kai shekara 35 suna aiki, ko kuma sun kai shekara 60 a duniya.

Idan zaku iya tunawa Ganduje ne ya umarci tsawaita wa’adin aiki a jihar, inda ma’aikata za su iya cigaba da aiki har na tsawon shekara biyar bayan sun kai lokacin ritaya.

Gwamna Abba ya soke wannan ƙudurin, sannan ya yi umarni a dawo da shekarun ritayar shekara 35 ana aiki ko kuma shekara 60 a rayuwa.

Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban Ma’aikatan jihar, Abdullahi Musa ya ce bayan an soke ƙudurin ne, aka kafa kwamiti domin kididdige adadin ma’aikatan.

“Bayan bincike ne kwamitinmu ya gano cewa kusan ma’aikata 4,000 suke cikin wannan tsarin, amma za su yi ritaya a 1 ga Disamban 2024. Wannan na nufin a ƙarshen watan Satumba za su miƙa takardar ajiye aiki.

Sai dai Abdullahi Musa ya ƙara da cewa gwamnati ta shirye maye gurbin da za su bari bayan sun yi ritayar.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *