Gwamnatin Kano ta yi Ala wadai da rahoton da Cibiyar Wale Soyinka kan zargi take ‘yancin faɗin albarkacin baki ga ‘yan jarida a jihar .

IMG 215010 291025 1761771023581

Gwamnatin Kano tana mutunta ‘yancin ‘yan jarida bisa doka da tsarin mulkin ƙasa.

Hakan na kunshe ne cikin wata tattaunawa da  manema labarai, wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da al’amuran cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana rahoton a matsayin “mara tushe balle makama,”

“Gwamnatinmu tana maraba da kowace irin suka muddin an gina ta bisa gaskiya da hujjoji. Amma ba za mu lamunci kirkirarren labari ba wanda manufarsa ita ce bata sunan gwamnati,” in ji Waiya.

Kwamishinan ya kara da cewa, gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya da kare ‘yancin ‘yan jarida da kungiyoyin farar hula kamar yadda duniya da su kansu yan jaridar suka shaida hakan.

Idan za a iya tunawa, a cikin rahoton Cibiyar Wale Soyinka mai taken “Shrinking Freedoms: 2024 Journalism and Civic Space Status Report”, an ambaci Jihar Kano a matsayin daya daga cikin jihohin da aka fi samun rahotannin take ‘yancin faɗin albarkacin baki na ‘yan jarida tare da jihohin Lagos da Abuja.

Sai dai a martanin sa, Kwamishina Waiya ya ce, “Rahoton ba shi da madogara, kuma an fitar da shi ne da wata manufa ta siyasa. Cibiyar ma bata da wakilai a jihohin Najeriya da ke tattara sahihan bayanai musamman a Kano.”

Ya kuma bayyana cewa, Gwamna Abba ya samu lambobin yabo da dama daga manyan jaridun ƙasar saboda kyakkyawar hulɗarsa da manema labarai.

Daga cikin su har da Leadership Newspaper, wacce ta karrama shi da matsayin Gwamnan da Ya Fice Wajen Cigaban Ilimi a Najeriya, da kuma African Leadership Magazine, wacce ta ba shi lambar yabo ta “African Governor of the Year for Good Governance.”

Waiya ya ce, “Wannan yana tabbatar da cewa Kano tana cikin jerin jihohi da ke mutunta aikin jarida a Najeriya. Hakan ne ma ya sa jaridun ƙasa ke ganin Gwamna Yusuf a matsayin shugaba mai karɓar ra’ayi da buɗaɗɗen tunani.”

Kwamishinan ya kuma tabbatar wa da al’umma cewar gwamnatin Kano gwamnati ce ta al’umma kuma don al’umma, don haka kofa a bude take ga masu son kawowa jihar Kano cigaba a ko ina.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *