Gwamnatin Kano Za Ta Rarraba Kayayyakin Haihuwa Kyauta Don Bunkasa Kiwon Lafiyar Mata Masu Juna Biyu.

IMG 20250227 WA0045

Hukumar kula da asibitocin jihar Kano ta sanar da shirin ta na rabon kayayyakin haihuwa kyauta a jihar Kano, a wani shiri na gwamnatin jihar na inganta kula da masu juna biyu da majinyata.

Shirin wanda Gwamna Abba ke jagoranta na da nufin samar da muhimman kayayyakin kiwon lafiya ga iyaye mata masu juna biyu da marasa lafiya ba tare da biyan sisin kobo ba.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kula da asibitocin jihar Kano Samira Suleiman ta fitar ta jaddada cewa gwamnatin jihar Kano ashirye take don inganta harkokin kiwon lafiyar al’umma a kokarin rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da kuma inganta harkokin kiwon lafiya baki daya.

A cewar Suleiman ta hanyar wannan shiri, gwamnati zata cigaba da tallafawa mata masu juna biyu da marasa lafiya masu fama da lalurori na yau da kullun, kamar irin su cutar sikila.

Kayan da za a Rarraba sun hadar da:

– Kwanson kayan tiyatar masu ciki CS: Guda 500 don tallafawa hanyoyin sashin fidar masu ciki

– Kwanson kayan Haihuwa: Guda 6,000 don taimakawa haihuwa lafiya

– Sinadaran Hydroxyurea ga masu fama da ciwon sikila: An kiyasta kudin sa a kan Naira miliyan 55, wannan maganin zai tallafa wa masu fama da cutar sikila.

A cewar Mai magana da yawun asibitin, Wannan shiri ya ginu ne a kan tsarin kula da lafiyar mata masu juna biyu kyauta da jihar Kano ta bullo da shi a shekarar 2001, wanda ya haifar da karuwar yawan zuwa mata masu juna biyu da haihuwa a cibiyoyin kiwon lafiya na jihar.

Gwamnatin jihar ta kuma kaddamar da makon kiwon lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai, da kuma kananan yara don bunkasa sakamakon kiwon lafiya ta hanyar rigakafi.

A cewar sanarwar, Hukumar Kulada asibitocin za ta sanar lokacin da za a fara kaddamar da rabon wadannan Muhimman kayayyaki domin amfanar masu bukata

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *