Kwamitin dawo da zaman lafiya da yaki da ayyukan daba da ta’ammali da miyagun kwayoyi na jihar Kano ya kai samame maboyar bata gari dake ramin ‘research’ a bulbula Gayawa karamar hukumar Ungogo da Kofar Wambai dake cikin birnin Kano inda aka kama wadanda ake zargi da ta’ammali da miyagun kwayoyi sama da 80.
Kwamitin wanda Gwamnatin jihar Kano ta kafa ya hada da gamayyar jami’an tsaro na ‘yansanda, NDLEA da DSS da Civil Defence da Vigilant group da sauransu.
Tun da fari, da ya ke zan tawa da wakilin jaridar Daily Nigerian, Shugaban kwamitin kuma Kwamishinan kimiyya da Fasaha Dakta Yusuf Kofar Mata, ya ce kwamitin ya yi nasarar kama masu tada hankalin al’umma a unguwannin Kofar Na’isa da Dan Agundi.
Acewar Kwamishinan an kama manyan wadanda ke haddasa rikicin su 8 kuma za a tabbatar da an mika su gaban shari’a domin karbar hukunci.
“A wannan dare sai da muka kama mutane 8 da makamansu kuma sanannu ne su ‘yan unguwa ne”
Shi ma a nasa jawabin, Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano , Ibrahim Bakori wanda ya jagoranci samamen ya ce sun samu nasara ne sakamakon hadin kai tsakanin dukkan bangarorin jami’an tsaro dake aiki a jihar.
“Wannan nasara hadin kai ne ya jawo haka, mun shiga lungu da sako na area din da muka je, kun ga yadda muka shiga unguwanni da ramuka muna debo bata gari a cikin rami , mun kama mutane mun mika su ga CID, wadanda daga baya za su yi hadin over zuwa ga NDLEA.”
Kwamishinan ya kara da cewa za a gudanar da bincike kafin gurfanar da Mutanen a gaban kotu.
Da ya ke, jawabi bayan kammala samamen, Shugaban Kungiyar ‘The Elevators Initiative for Community Peace’, Mansur Kurugu ya yaba da yadda jami’an tsaron suka gudanar da samamen, sannan yayi kira da a dauki matakan gyara tarbiyar matasan baya ga amfani da karfi.



Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD