
Alfijr ta rawaito Gwamnatin Najeriya ta sanar da dage kidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023 da aka shirya gudanarwa a ranar 29 ga watan Maris 2023.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa karshen taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Laraba a Abuja.

A cewar ministan, matakin da aka dauka na sauya lokacin kidayar ya biyo bayan dage zaben gwamnoni da na majalisar jiha da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi daga ranar 11 ga watan Maris zuwa 18.
Ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da Naira biliyan 2.8 domin sayo wasu manhajoji da za a yi amfani da su wajen gudanar da kidayar jama’a.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
Allahamdulillah Allah yasa muna raye
Allah yasa mudace