Gwamnatin Najeriya ta ayyana  ranakun hutun  bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara

FB IMG 1723115651747

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Laraba 25, da Alhamis 26 ga Disamba, 2024, da kuma Laraba 1 ga Janairu, 2025 a matsayin ranakun hutu don bukukuwan Kirsimeti, Ranar  da sabuwar shekara.

Alfijir labarai ta rawaito ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a cikin wata sanarwa da babban sakatariyar ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Litinin.

Tunji-Ojo ya mika sakon gaisuwa ga daukacin al’ummar Najeriya, inda ya bukace su da su yi amfani da lokacin bukukuwan domin yin Addu’oi dan nuna  kimar soyayya, zaman lafiya da hadin kai baki daya musamman a sabuwar shekara.

Sannan ya jaddada mahimmancin lokacin a matsayin lokacin da za a samar da jituwa da karfafa zumunci a tsakanin iyalai da al’ummomi baki daya.

Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da ci gaban kasa domin ci gaban kasa.

Lokacin Kirsimeti lokaci ne mai kyau don tunani na ruhaniya da sabunta ƙasa. Yayin da muke murnar zagayowar ranar haihuwar Yesu, Sarkin Salama, mu nuna alheri tare da kyautatawa juna, ba tare da la’akari da bambancin da ke tsakaninmu ba,” in ji Tunji-Ojo.

Ya kuma baiwa ‘yan kasar tabbacin ci gaba da kudirin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da wadata a fadin kasar nan.

Yayin da yake yi wa ‘yan Nijeriya fatan alheri da bukukuwan Kirsimeti da kuma samun ci gaba a shekarar 2025, Ministan ya bayyana kwarin gwiwar sa kan manufar sabunta bege na Gwamnatin Shugaba Tinubu da ke kawo sabuwar shekara, ingantacciyar tattalin arziki da wadata da za ta zama kishin duniya.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *