Gwamnatin Najeriya ta baiwa dalibar da ta lashe gasar Ingilishi ta duniya kyautar dubu 200

IMG 112946 29825 1756463403178

Gwamnatin Tarayya ta baiwa Nafisah Abdullahi, wadda ta lashe gasar TeenEagle Global Finals, kyautar N200,000.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya mika wannan lambar yabo a wani biki da aka gudanar a Abuja.

A baya-bayan nan, Atiku Foundation ta baiwa zakarun gasar TeenEagle — Nafisa Abdullahi, Rukaiya Fema da Khadija Kalli — guraben karatu da aka dauki nauyinsu saboda bajintar da suka nuna a gasar TeenEagle Global Finals.

Wadannan ‘yan mata, wadanda suka fito a matsayin zakarun duniya a fannoni daban-daban na gasar, sun samu yabo daga gudauniyar saboda abin da ta kira “nasara mai ban mamaki.”

Daga cikin wadanda suka samu wannan yabo akwai Nafisa Abdullahi ‘yar shekara 17, wadda ta fito fili saboda kwarewarta a harshen Ingilishi, tunani mai zurfi da kuma iya bayyana magana, abubuwan da suka taimaka mata wajen doke mahalarta daga kasashe 69.

Sai dai an jiyo Hajiya Fatima Muhammad tace mnistan ilimi ne a aljihunsa ya baiwa yarmu naira 200,000 ba Tinubu ba .

Daga daga cikin mahaifiyar yan mata ukun da suka yi nasara a gasar Turanci ta duniya da aka gudanar a Ingila Hajiya Fatima Muhammad Mairiga yace kuɗin da aka baiwa yaransu, ministan ilimi na kasa ne ya bayar a aljihunsa ba daga asusun gwamnatin tarayya ba.

Hajiya Fatima Muhammad wacce itace mahaifiyar Rukayya Muhammad Fema tana wannan batu ne bayan cece kuce yayi yawa a kafafen sada zumunta kan kyautar naira dubu dari biyu da ake cewa gwamnanatin Tinubu ta baiwa Nafisa Abdullahi da tayi nasara a gasar Turanci ta duniya.

Fatima tace ministan ne da kansa yayi Wannan kyauta domin karrama daliban guda uku.

A wani faifen bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta na zamani wanda TST Hausa ta yi nazari akansa ,anga yadda Fatima Muhammad Mairiga ke cewa bayan ministan ya baiwa Nafisa Abdullahi naira 200,000 ya kuma baiwa Rukayya Muhammad Fema da Khadija Ibrahim Kalli naira 100,000 ko waccensu.

“Maraina kadan barawo ne ,wannan ce kallamar da ta fito daga bakin Fatima Muhammad Mairiga mahaifiyar Rukayya Muhammad Fema”

Sai dai fa duk da haka an shiga cece-kuce a Arewa musamman a shafukan sada zumunta na zamani bayan da gwamnatin tarayya ta baiwa, Nafisa Abdullahi, kyautar kuɗin naira 200,000 a matsayin karramawa bisa nasarar da ta samu a gasar ƙasashen duniya na Ingilishi koda kuwa ministan ne ya bayar wasu na ganin abin kunya ne.

Wasu na ganin kuɗin ko minitan ne ya bayar sun yi kadan idan aka kwatanta da rawar da ta taka wajen wakiltar Najeriya a idon duniya.

A cewar su, bai dace a takaita irin wannan babbar nasara a kan naira dubu ɗari biyu ba, alhali gwamnati na kashe kuɗaɗe masu yawan gaske a wasu fannoni.

Sai dai wasu kuma sun bayyana cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne karramawar kanta, ba lallai sai adadin kuɗin ba.

A ganinsu, wannan alama ce ta yabo da kuma girmamawa daga gwamnatin tarayya ga jarumar, kuma hakan na iya ƙarfafa sauran matasa su yi ƙoƙari a fannoni daban-daban.

Masu sharhi sun ce wannan cece-kuce na nuna yadda jama’a ke da bambancin fahimta a kan yadda gwamnati ke karrama ‘yan Najeriya da suka yi fice a fagen ilimi, wasa ko al’adu.

A halin yanzu, tattaunawar na ci gaba da ƙara zafi a shafukan sada zumunta, inda jama’a ke bayyana ra’ayoyinsu kan darajar kyautar da kuma tasirin ta ga ci gaban matasan Arewa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *