Da yake bayanin nadin lokacin da suka kawo ziyara fadar Sarkin dake Gidan Nassarawa Babban mai tsare tsare na ƙasa da kuma mataimakin Shugaban kula da fasaha a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya yace an nada Sarkin ne bisa Cancantarsa da kuma da cewa da bashi Jagorancin.
A wata sanarwa Mai dauke dasa hannun Sakataren Yada Labaran Sarkin Abubakar Balarabe Kofar Naisa Yace jagoran tawagar yayi bayanin cewar Kwamitin ciyarwar bana siyasa bane illa dai kawai na Gwamnatin Tarayya domin hidimtawa al’uma.
Ya kara da cewa aikin kwamitin zai rabar da kayan abinci da suka hada da Shinkafa da Gero da kuma Man girki.
Yace a shekarun baya aikin Kwamitin ciyarwar ya takaita ne ga tara shugabanni domin yin breakfast da shugaban Kasa kawai, amma yanzu shugaba Bola Tinubu yayi umarnin a kara fadadawa zuwa bayar da kayan abincin a dukkanin shiyoyin Najeriya guda shida.
Sauran Yan Kwamitin dai sun hada Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya da Daraktotoci da Sanatoci da ‘Yan majalisun Tarayya duk a karkashin kulawar ofshin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Tawagar karkashin Babban mai tsare tsare na kasa tayi fatan samun dukkan nasara daga Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a wannan jagoranci da aka bashi.
Da yake jawabi Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yabawa gwamnatin Tarayya bisa wannan tsari data fadada na ciyarwa a wannan wata mai albarka.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya godewa Allah tareda fatan wannan tsari da aka shigo dashi zai zama mai dorewa domin taimakawai al’uma.
Yace yana fatan wadanda aka saka a cikin Kwamitin zai kawo gyara da cigaba tareda wadanda akayi abun domin su zasuci amfaninsa.
Ya godewa Gwamnatin Tarayya data bashi wannan dama domin yiwa al’umar kasa hidima tareda tabbatar da cewa zasuyi duk mai yuwuwa domin samun nasarar aikin da aka basu.
Ya tabbatar da cewar zasuyi duk abunda ya kamata tareda bada shawarwari da duk wata gudunmawa domin tabbatar da nasarar kwamitin.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t