Gwamnatin Najeriya ta sanar da ranar hutun murnar haihuwar Annabi Muhammad S A W

IMG 105658 03925 1756893433206

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa ranar Juma’a, 5 ga Satumba, 2025, za ta kasance hutu ga ma’aikatan Najeriya domin bikin Mauludi na ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar cikin gida, Dakta Magdalene Ajani, ya fitar a madadin Ministan ma’aikatar.

Sanarwar ta taya musulmi a Najeriya da kasashen duniya murna, tare da kira da su yi koyi da halayen Annabi na zaman lafiya,da ƙauna,da tawali’u, haƙuri da jin ƙai.

Haka kuma, sanarwar ta bukaci ‘yan Najeriya daga addinai daban-daban da su yi amfani da wannan dama wajen roƙon Allah ya kawo zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a ƙasar, tare da goyon bayan ƙoƙarin gwamnati na haɗin kai da cigaba.

Ministan cikin gidan ya yi fatan musulmi za su gudanar da bikin Maulud cikin farin ciki da lumana.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *